Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II

Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II

Hukumar yaki da rashawa da karben koke koke ta jahar Kano a karkashin jagorancin Muhyi Magaji Rimin Gado ta shawarci gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje daya dakatar da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.

Hukumar ta bayyana haka ne cikin rahoton wucin gadi data buga kuma ta mika ma kamfanin dillancin labaru, NAN, inda tace hakan ya zama wajibi sakamakon katsalandan da rashin basu hadin kai da Sarkin yake nunawa a binciken da suke yi game da zargin batar da naira biliyan 3.4 a fadar Sarkin.

KU KARANTA: Likafa ta cigaba: An samu zababben Sanata dan Kwankwasiyya a kasar Gambia

Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II

Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II
Source: UGC

Hukumar na tuhumar Sarkin Kano da fadar masarautar Kano da hannu cikin yin bindiga da kudaden fadar da suka kai naira miliyan dubu uku da miliyan dari hudu daga shekarar 2014 zuwa 2017, wanda daga ciki take zargin an sace naira biliyan 1.4 ne na kudin.

Haka zalika hukumar ta zargi Sarkin da kashe naira biliyan 1.9 don amfanin kansa, wanda hakan ya nuna akwai lauje cikin nadi game da kashe wadannan makudaden kudaden al’umma, kuma hakan ya saba ma sashi na 120 na kundin dokokin Najeriya na shekarar 1999, da kuma sashi na 8 na dokokin masarautar Kano.

Bugu da kari Legit.ng ta ruwaito hukumar na cewa laifin ya saba ma sashi na 314 na kundin hukunta manyan laifuka, da kuma sashi na 26 na kundin dokokin hukumar yaki da rashawa da karben koke koke ta jahar Kano.

“Haka zalika muna da tabbacin Sarki Muhammadu Sunusi II yana kawo mana cikas a binciken da muke yi ta hanyar umartar yan fadarsa da muka gayyata domin bincikensu da kada su amsa gayyatarmu, wanda hakan ya saba ma sashi na 25 na dokokinmu.” Inji rahoton,

Don haka hukumar ta nemi Gwamna Ganduje daya dakatar da Sarkin Kano da dukkanin wadanda take tuhuma daga mukamansu har sai ta kammala gudanar da bincikenta, domin ta samu damar gudanar da bincikenta ba tare da wani tasgaro ba.

A hannu guda hukumar ta shawarci gwamnnan daya soke kwangilar yin kwaskwarima ga Babban Daki, Kofar Kudu da Gidan Sarki Dorayi da Sarkin Kano ya baiwa kamfanin Tri-C, saboda kamfanin mallakin babban hadimin Sarkin ne, Alhaji Mannir Sunusi, guda daga cikin wadanda take binicka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel