Dakarun MNJTF sun kashe 'yan kungiyar ISWAP 20

Dakarun MNJTF sun kashe 'yan kungiyar ISWAP 20

A cigaba da atisayen kakkabe 'yan kungiyar IS reshen Afrika ta yamma (ISWAP) daga kasashen gefen tekun Chadi, dakarun rundunar sojin hadin gwuiwa na kasashen gefen tekun Chadi (MNJTF) sun kai wani samame tare da kashe mayakan kungiyar 20.

Dakarun sun kashe mayakan kungiyar ne a wani harin bazata da suka kai a yankin Arege, Malkonory da Tumbum Rego.

Hakan na kunshi ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar MNJTF, Kanal Timothy Antigha, ya fitar a ranar Litinin.

Kanal Antigha ya ce sun lalata motocin yaki da makamai da alburusai da sinadarai masu fashe wa na mayakan kungiyar.

Dakarun MNJTF sun kashe 'yan kungiyar ISWAP 20

Dakarun MNJTF
Source: Depositphotos

Kazalika ya bayyana cewar dakarun MNJTF hudu sun samu raunka yayin gumurxun da aka yi kafin a kashe mayakan.

DUBA WANNAN: Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare (Hotuna)

Ya kara da cewa rundunar MNJTF a shirye take wajen sauke nauyin dake kan ta na tabbatar da tsaron a sassan kasashen gefen tekun Chadi tare da neman goyon bayan jama'ar yankin kasashen gefen tekun Chadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel