Biyu babu: APC ta kori tsohon gwamna Yari daga jam'iyyar

Biyu babu: APC ta kori tsohon gwamna Yari daga jam'iyyar

Jam'iyyar APC mai mulki ta kori tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari tare da mataimakin jam'iyyar na yankin arewa, Lawal Shu'aibu.

APC ta kori Yari tare Lawal ne bisa zarginsu da hada baki tare da yiwa jam'iyyar kafar sagegeduwar rasa kujerunsu da suka lashe a zabukan da aka gudanar.

Jam'iyyar ta cimma wannan matasaya ne bayan wani zaman gaggawa da shugabanninta da masu ruwa da tsaki suka yi a jihar Zamfara da yammacin ranar Litinin.

Biyu babu: APC ta kori tsohon gwamna Yari daga jam'iyyar

Tsohon gwamna Abdulaziz Yari
Source: UGC

Sanarwar korar Yari da Lawal na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Surajo Garba Mai Katako, ya rattaba wa hannu, inda a cikin sanarwar ya bayyana cewar sun yanke shawarar korar su ne saboda sun hada kai wajen haifar da cikas din da ya kai ga asarar kujerunta da jam'iyyar ta tafka a jihar.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga ba su kai min hari ba, samame na kai mafakarsu - Gwamnan Zamfara

A makon jiya ne kotun koli ta rushe dukkan zababbun 'yan takarar jam'iyyar APC a jihar Zamfara tare da umartar hukumar zabe ta kasa (INEC) ta kwace takardar shaidar cin zaben dukkan 'yan takarar jam'iyyar a dukkan zabukan da aka kammala. Kazalika kotun ta bayyana jam'iyyar PDP, wacce ta zo ta biyu, a matsayin wacce ta lashe ta zabukan kujerun jihar Zamfara.

Kotun ta rushe 'yan takarar APC ne bayan samun jam'iyyar da laifin kin gudanar da zaben fidda 'yan takara bisa gwadaben doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel