Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin dakaru a jihar Borno

Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin dakaru a jihar Borno

A yanzu din nan a nemi kwamanda da kuma sojoji shida biyo bayan aukuwar wani mummunan hari da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta kai wasu sansanan dakaru biyu cikin jihar Borno a ranar Asabar.

A yayin da aka tabbatar da mutuwar wani dakarun soja guda daya bayan da mayaka suka hautsuna sansanan dakarun a jihar Borno, binciken jaridar Premium Times ya tabbatar da cewa harin ya janyo wa rundunar sojin asarar makamai masu tarin yawa da babu misali.

Mayakan Boko Haram sun yiwa sansanin dakaru na bataliya mai lamba 192 kuli-kulin kubura a kauyen Delwa daura da hanyar Maiduguri zuwa Damboa a karamar hukumar Konduga, kazalika sun kwatanta wannan ta'addanci kan bataliyar soji mai lamba 242 a karamar hukumar Marte.

Akwai yiwuwar tabbatar da cikakken shiri daga bangaren mayakan Boko Haram yayin da suka zartar da harin a lokaci guda da misalin karfe 6.00 na Yammacin Asabar.

KARANTA KUMA: Jinjirin watan Shawwal ya bayyana a kasar Saudiya

Wannan hari na zuwa ne biyo bayan aukuwar wani mummunan hari da mayakan Boko Haram suka kai sansanin dakaru a ranar 22 ga watan Mayu cikin karamar hukumar Gubio ta jihar Borno. Harin ya salwantar da rayuwar soja guda daya tare da jikkatar wasu guda uku.

Majiyar rahoton ta ruwaito cewa, duk da ci gaba da aukuwar wannan munanan hare hare, shugaban hafsin sojin kasan Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai a ranar Alhamis ta makon da ya gabata ya bayyana cewa, tuni aka samu babbar galaba ta cin nasara akan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel