Ki dunga jan hankalin maigidanki idan kun zo wajen kwanciya – Obasanjo ga Aisha Buhari

Ki dunga jan hankalin maigidanki idan kun zo wajen kwanciya – Obasanjo ga Aisha Buhari

- Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yace uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, tayi namijin kokari da ta bayyana gazawar gwamnatin maigidanta

- Obasanjo ya bukaci Aisha da ta dunga tadi da maigidan nata idan sun zo kwanciya don jan hankalinsa akan abubuwan da ke wakana a kasar

- A kwanan nan ne Aisha ta caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma tsarinta na magance lamarin ta’addanci a yankin arewacin kasar

Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yace uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, tayi namijin kokari da ta bayyana wuraren da gwamnatin maigidanta ta gaza.

A kwanan nan ne Aisha ta caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma tsarinta na magance lamarin ta’addanci a yankin arewacin kasar.

Don haka a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, Obasanjo ya bukaci Aisha da ta dunga tadi da maigidan nata idan sun zo kwanciya a matsayin hanyar jan hankalin Shugaban kasar domin sanar dashi rashin jin dadinta akan abubuwan da ke wakana a kasar.

A wani jawabi daga hadiminsa, Kehinde Akinyemi, Obasanjo yayi maganar ne lokacin da ya taka rawar mai masaukin baki na hukumar tantancewa na wata kafar sadarwa, wato Penpushing Media a dakin karatunsa na Abeokuta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Boko Haram sun karbe wani gari a Borno

Ya jinjina wa uwardidar Shugaban kasar, cewa matsayarta abune mai kyau ga ci gaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel