Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta fatattaki Sanata Marafa da Wakkala

Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta fatattaki Sanata Marafa da Wakkala

Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta fatattaki wakilin shiyyar Zamfara ta Tsakiya a zauren majalisar dattawa, Sanata Kabiru Marafa bisa zargin sa da aikata miyagun laifuka na nuna rashin goyon baya da suka sabawa akida ta jam'iyyar sa.

Bisa zargin aikata kwatankwacin wannan laifi, jam'iyyar ta kuma fatattaki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mallam Ibrahim Muhammad Wakkala da kuma dan majalisar tarayya mai wakilcin kananan hukumomin Kauran Namoda da kuma Birnin Magaji, Aminu Jaji.

Cikin sanarwar da sakataren jam'iyyar ya bayyana a madadin shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara, Shehu Isa, ya ce wannan hukunci na fatattakar jiga-jigan jam'iyyar uku ya bayu ne yayin wani taron kusoshin jam'iyyar da aka gudanar a ranar Lahadi cikin birnin Gusau.

Sakataren hulda da al'umma na jam'iyyar ya ce tanadin sashe na 21 cikin kundin tsarin jam'iyyu na Najeriya yayi tasiri wajen yanke hukuncin fatattakar jiga-jigan jam'iyyar uku a sakamakon laifukan da suka aikata na juya wa jam'iyyar su baya.

KARANTA KUMA: ASUU ta nemi shugaba Buhari ya bayyana shaidar hakkin Malaman jami'o'i a cikin kasafin kudin 2019

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, cikin wata rubutacciyar wasika da ta aike da ita a ranar Litinin, jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta ankarar shugaban jam'iyyar na kasa Kwamared Adams Oshiomhole, dangane da wannan hukunci da ta zartar akan jiga-jigan ta guda uku.

Ana iya tuna cewa jam'iyyar APC ba ta hurumi na rikon kowace kujerar siyasa a jihar Zamfara biyo bayan hukuncin da kotun kolin kasar nan ta zartar ta na soke zaben fidda gwanayen takara tare da haramta masu dukkanin 'yan takarar nasarorin su na lashe zaben kasa da aka gudanar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel