Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare (Hotuna)

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare (Hotuna)

Rundunar 'yan sanda ta musamman karkashi gwarzon dan sanda, Abba Kyari, ta yi nasarar cafke dilolin dake shigo da muggan makamai Najeriya daga kasashen Libya da Burkina Faso.

Masu laifin sun amsa cewar suna sayar da makamai ga 'yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Sun bayyana hakan ne yayin da aka yi bajakolinsu a hedikwatar rundunar 'yan sanda dake Abuja a ranar Litinin.

Kazalika, sun bayyana cewar suna shigo da makamai zuwa Najeriya ne ta kan iyakokinta da kasashen Nijar da Benin.

Daga cikin makaman da aka kama a wurin dilolin akwai carbi 600 na alburushin bindigar AK47 da kuma manyan bindigogi samfurin AK47 da wasu kananu.

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare (Hotuna)

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare
Source: Facebook

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare (Hotuna)

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai
Source: Facebook

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare (Hotuna)

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su
Source: Facebook

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare (Hotuna)

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su
Source: Facebook

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare (Hotuna)

Rundunar Abba Kyari ta kama muggan makamai da masu safarar su daga kasashen ketare
Source: Twitter

Kazalika rundunar ta bayyana cewar ta yi nasarar kama masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami 38.

Ko a ranar Lahadi, Legit.ng ta kawo muku labarin cewar Dakarun sojin Najeriya na rundunar atisayen HARBIN KUNAMA III sun yi nasarar kama wasu 'yan bindiga dake satar mutane domin garkuwa da su da kuma aikata fashi da makami.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga ba su kai min hari ba, samame na kai mafakarsu - Gwamnan Zamfara

Rundunar sojin ta kama mutanen ne yayin wani atisaye da ta gudanar a kauyen Sheme da hanyar zuwa dajin Ruwan Godiya da makwabatan kauyaka dake karkashin karamar hukumar Faskari.

A sanarwar da kanal Sagir Musa, mukaddashin darektan yada labaran rundunar soji, ya fitar a shafin rundunar soji dake 'facebook', ya ce dakarun soji sun gudanar da atisaye a kauyen ne bayan samun sahihan bayanan sirri a kan aiyukan 'yan ta'addar da suka addabi kananan hukumomin Funtua da Faskari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel