Cin hanci: Kotu ta yanke wa toshon shugaban NIMASA hukuncin daurin shekaru 7

Cin hanci: Kotu ta yanke wa toshon shugaban NIMASA hukuncin daurin shekaru 7

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake zamanta a jihar Legas ta yanke wa tsohon shugaban hukumar NIMASA, Calistus Obi, daurin shekaru 7 a gidan yari bayan samun sa da laifin badakalar miliyan N136.

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ce ta gurfanar da Obi bisa tuhumarsa da badakalar miliyan N136.

An nada Obi a matsayin mukaddashin shugaban hukumar NIMASA watanni biyu bayan shugaba Buhari ya hau mulki a shekarar 2015.

Buhari bai dade da hawa mulki ba ya kori shugaban hukumar NIMASA Patrick Akpobolokemi.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Akpobolokemi a gaban kotu bisa tuhumarsa da badakala.

Ana cikin sauraron karar Akpobolokemi ne hukumar EFCC ta kara gurfanar da Obi bisa gano wata badakalar kudi da ya tafka a shekarar 2014.

Cin hanci: Kotu ta yanke wa toshon shugaban NIMASA hukuncin daurin shekaru 7

Cin hanci: Kotu ta yanke wa toshon shugaban NIMASA hukuncin daurin shekaru 7
Source: UGC

A cikin watan Mayu ne alkalin kotun, Jastis Mojisola Olatoregun, ya bayyana tabbatar da samun Obi da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

DUBA WANNAN: Majalisar wakilai: Ba zan taba janye wa Gbajabiamila ba - Dan majalisar APC

Takardar tuhumar da ake yi wa Obi ta nuna cewar ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi tun a cikin watan Agusta na shekarar 2014.

A cewar hukumar EFCC, Obi tare da tsohon shugaban ma'aikatan hukumar NIMASA sun hada baki tare da wawure wasu miliyoyi masu yawan gaske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel