ASUU ta nemi shugaba Buhari ya bayyana shaidar sanya hakkin Malaman jami'o'i a cikin kasafin kudin 2019

ASUU ta nemi shugaba Buhari ya bayyana shaidar sanya hakkin Malaman jami'o'i a cikin kasafin kudin 2019

Duk da kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta janye yajin aikin sai mama ta gani da ta afka a watan Nuwamban 2018, amma har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawarin da ta dauka na yarjejeniyar da suka kulla ta janye yajin aikin.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin ne a ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata domin matsawa gwamnati lamba kan inganta albashi da kudaden alawus na malamai da kuma farfado da darajar jami'o'in kasar nan.

Sai dai har ila yau gwamnatin ba ta cika alkawarin ta ba na biyan ragowar alawus din malamai har kimanin Naira biliyan ashirin da biyar. Kungiyar ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayyana mata shaidar sanya wannan hakki na malamai a cikin kasafin kudin kasa na 2019.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa Farfesa Biodun Ogunyemi, shi ne ya shigar da wannan muhimmiyar bukata yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi cikin birnin Ilorin na jihar Kwara.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku ya zargi fadar shugaban kasa da kawo jinkiri a kotun daukaka kara

Duk da cewar a baya kungiyar ASUU ta gindaya sharadin koma wa yajin aiki idan har gwamnatin Tarayya ta ki mutunta yarjejeniyar da suka sanya wa hannu, Farfesa Biodun ya ce a halin yanzu ba bu wannan batu a kasa illa iyaka shugaba Buhari ya nuna hali na dattako.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel