Zaben 2019: Atiku ya zargi fadar shugaban kasa da kawo jinkiri a kotun daukaka kara

Zaben 2019: Atiku ya zargi fadar shugaban kasa da kawo jinkiri a kotun daukaka kara

A yayin ci gaba da kalubalantar sakamakon babban zaben kasa na 2019, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gano wani bakin tuggu da fadar shugaban kasa ke kullawa domin cin galaba a kansa a gaban kotun daukaka kara.

Atiku da kungiyar sa ta kwararrun lauyoyi na ci gaba da zargin fadar shugaban kasa da kawo jinkirin fara sauraron karar sa ta kalubalantar sakamakon zaben kasa domin cimma manufa ta watsi da karar sa.

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya shigar da koken sa a gaban shugabar kotun daukaka kara, Jastis Zainab Bulkachuwa, kan kawo jinkiri gabanin fara sauraron karar sa ta kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya shigar da korafin sa cikin wata rubutacciyar wasika ta ranar 31 ga watan Mayun 2019 da sanadin daya daga cikin lauyoyin sa, Silas Joseph Onu, da ya ce hakan na zuwa ne da umurnin jagoran kungiyar su ta lauyoyi, Levi Uzokwu.

KARANTA KUMA: Sa'a 1 kacal jaririyar ki za tayi a duniya - Likitoci sun shaidawa wata Mata bayan ta sauka

Ko shakka babu an samu jinkirin ci gaba da shirye-shiryen fara sauraron karar Atiku ta kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa yayin da babbar Alkaliya mai shari'a, Zainab Bulkachuwa ta zame hannu ta daga shari'ar.

Legit.ng ta fahimci cewa, domin tsarkake kanta daga tantamar nuna wariya ko kuma rashin gaskiya, Jastis Bulkachuwa ta zame hannun ta kwanaki 11 da suka gabata biyo bayan nasarar mai gidanta ta lashe kujerar Sanatan shiyyar Bauchi ta Arewa a karkashin jam'iyya mai ci ta APC.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel