Jihar Zamfara ta kaddamar da hukuncin kisa kan masu yiwa yan bindiga leken asiri

Jihar Zamfara ta kaddamar da hukuncin kisa kan masu yiwa yan bindiga leken asiri

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana cewa gwamnatin jihar nan ba da dadewa ba zata soma zartar da hikuncin kisa akan majiyan yan bindiga a jihar.

Gwamnan ya bada sanarwan ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, lokacin da ya ziyarci kauyen Lilo a yankin Wonkana dake karamar hukumar Gusau a jihar.

Ya kai ziyara kauyen ne don ta’aziyya ga al’umman bisa harin da yan bindiga suka kai kauyen a daren Asabar, wanda yayi sanadiyar mutuwan mutane takwas da kuma raunata mutane 18.

Yace gwamnatinsa ta samar da kayan aiki ga hukumomin tsaro don gudanar da ayyukan su a tsanaki.

Da farko, sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, ya mika godiya ga gwamnan bisa ziyaran kuma yayi kira ga goyon bayan gwamnati da hukumomin tsaro wajen magance matsalan.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga ba su kai min hari ba, samame na kai mafakarsu - Gwamnan Zamfara

Bello ya roki al’umman kauyen da su cigaba do goya ma gwamnati baya tare da addu’ar nasara wajen yaki da ta’addanci.

Gwamnan ya bada gudumuwar miliyan biyar ga iyalan wadanda lamarin ya cika da su, ya kuma umurce su da su je ofishin Sakataren Gwamnatin jihar don daukan nauyin wadanda suka ji rauni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel