Musulmai a kasar Mali sun yi bikin karamar sallah a yau Litinin

Musulmai a kasar Mali sun yi bikin karamar sallah a yau Litinin

A safiyar yau Litinin, 3 ga watan Yuni ne al’umman Musulmi na kasar Mali suka yi bikin karamar salla, bayan sun samu tabbacin ganin jaririn watan Shawwal a yammacin ranar ahadi, 2 ga watan Yuni.

Hakan na nufin sun kai karshen azumin Ramadana a ranar Lahadi, sannan yau Litinin yayi dai-dai ga farkon watan Shawwal.

A wata sanarwa dauke da sa hannun ministan harkokin addini na kasar zuwa ga kafofin watsa labarai na kasar, Gwamnati ta tsaida ranar Litinin 3 ga watan Yuni a matsayin ranar karamar Sallah a fadin kasar Mali."

Sanarwar ta Ambato ministan na cewa an ga watan a wasu wurare na wasu yankunan kasar, kamar Kati da kuma Bamako fadar gwamnatin kasar.

Dan haka sanarwar ta ce ya zamo wajibi a yi sallah ranar ta Litanin a fadin kasar baki daya.

Al'ummar kasar ta Mali dai sun dauki azumin Ramadan ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu sabanin yadda akasarin kasashen musulmi a fadin duniya suka tashi da azumin ranar Litanin.

KU KARANTA KUMA: Mazan Kirista su auri mata sama da guda daya, babu ayar Injila da ya haramta hakan - Fasto

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta kaddamar da Talata, 4 ga watan Mayu da Laraba, 5 ga watan Mayu a matsayin ranakun hutu domin bikin karamar sallar.

Sakatariyar din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Barista Georgina Ekeoma Ehuriah ta sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu ta hannun Daraktan labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Mohammed Manga.

Ta taya Musulmai murnar kammala azumin Ramadana cikin nasara sannan ta bukaci dukkanin yan Najeriya da suyi amfani da bikin wajen addu’an zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da daidaitar kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel