Ba tare da wata wata ba, El-Rufai ya nada mutane 17 a gwamnatinsa

Ba tare da wata wata ba, El-Rufai ya nada mutane 17 a gwamnatinsa

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sake nada wasu manyan jami’an gwamnatinsa bisa mukamansu, mukaman da suka rike a wa’adin mulkinsa na farko, kamar yadda fadar gwamnatin jahar Kaduna ta sanar.

Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya mayar da sakataren gwamnati, Balarabe Abbas Lawal bisa mukaminsa, kamar yadda yayi ma babban sakatarensa, Dakta Salisu Suleiman da kuma babban mashawarcinsa Jimi Lawal.

KU KARANTA: El-Rufai ya bayyana muhimmin rawar da Buhari ya taka wajen zaben Gbajabiamila

Ga dai cikakken jerin jami’an gwamnatin jahar Kaduna da gwamnan ya mayar kan mukamansu da suka hada da;

1. Balarabe Abbas Lawal sakataren gwamnati

2. Dr. Salisu Suleiman babban sakataren gwamna

3. Jimi Lawal babban mashawarci

4. Peter Jones mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati

5. James Kanyip mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati

6. Zainab Mohammed babbar hadimar gwamna akan tattalin arziki

7. Adejoh Momoh mataimakin gwamna akan bincike da tattara bayanai

8. Joel Adoga mataimaki na musamman akan sha’anin mulki

9. Mubarak Mohammed mataimaki na musamman akan gudanar da manyan ayyuka

10. Hosea Sani mataimaki na musamman akan hukumar KADGIS

11. Maimuna Zakari mataimakiya ta musamman wajen ayyuka masu muhimmanci

12. Halima Idris mataimakiya ta musamman akan kirkire kirkire

13. Tamar Nandul mataimaki na musamman akan alakar gwamnati da gwamnati

14. Peculiar Nwaohiri mataimaki na musamman a ofishin Kaduna dake Abuja

15. Elias Yahaya mataimaki na musamman akan hidindimu

16. Iliyasu Jega mataimaki na musamman akan Protocol

17. Umar Farouk Saleh hadimin gwamna

Daga karshe sanarwar ta umarci dukkanin sauran manyan mashawartan gwamnan su cigaba da aikinsu har zuwa karshen wa’adin majalisar dokokin jahar, haka zalika tace za’a bayyana sauran sunayen jami’an gwamnati amma sai bayan an rantsar da yan majalisun dokokin jahar Kaduna

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel