Majalisar wakilai: Ba zan taba janye wa Gbajabiamila ba - Dan majalisar APC

Majalisar wakilai: Ba zan taba janye wa Gbajabiamila ba - Dan majalisar APC

Olajide Olatubosun, mamba a majalisar wakilai daga jihar Osun kuma dan jam'iyyar APC, ya ce majalisar su na fuskantar barazanar rasa 'yancinta.

Da ake magana da manema labarai a Abuja, Olubatosun, mai takarar neman zama shugaban majalisar wakilai, ya ce zai yaki cushe da dashen 'yan takarar da dukkan karfinsa.

Jam'iyyar APC ta mika kujerar shugabancin majalisar wakilai zuwa yankin kudu maso yamma kuma ta nuna Femi Gbajabiamila, mamba a jam'iyyar daga jihar Legas, a matsayin dan takarar da take so a zaba.

Olatubosun ya ce sashe na 50 a karkashin karamin sashe na 1b na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 1999 ya bawa mambobin majalisar wakilai damar zaben daya daga cikinsu dake da gogewa a majalisa domin ya zama shugaban majalisa.

Majalisar wakilai: Ba zan taba janye wa Gbajabiamila ba - Dan majalisar APC

Olajide Olatubosun
Source: UGC

"Cikakken dan jam'iyya ne ni kuma zan kasance mai biyayya ga umarninta matukar babu saba wa kundin tsarin mulkin kasa a ciki," cewar sa.

Sannan ya cigaba da cewa; "ina da gogewa a majalisa kuma na cancanta, a saboda haka ba zan janye takara ba saboda wani dan takarar."

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga ba su kai min hari ba, samame na kai mafakarsu - Gwamnan Zamfara

Dan majalisar ya kara da cewa kundin tsarin mulki ya yi magana a kan bangaren gwamnati guda uku da kuma aikin kowanne daga cikinsu tare da koka wa a kan yadda bangaren zartar wa ke shiga harkokoin majalisa tun shekarar 1999, lamarin da ya ce ya zama barazana ga 'yanci da ma wanzuwar majalisar baki daya.

Kazalika ya bayyana cewar ya na da abokai a ragowar jam'iyyun dake da mambobi a majalisar, wadanda ya ce ya na da tabbacin zasu goya masa baya yayin zaben shugaban majalisar da za a yi a cikin wannan watan na Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel