Taron OIC: Kungiyar matasan Igbo sun caccaki Ohanaeze akan kira ga Buhari yayi murabus

Taron OIC: Kungiyar matasan Igbo sun caccaki Ohanaeze akan kira ga Buhari yayi murabus

- Kungiyar matasan Igbo tayi Allah wadai da kiran da kungiyar Ohanaeze tayi na neman Buhari yayi murabus biyo bayan sukar halartan taron OIC da yayi a kasar Saudiyya

- A cewar kungiyar, “rashin hankali da jahilci ne”zai sa wani ya nemi Buhari yayi murabus ta hanyar amfani da sunan kungiyar Igbo

- Kungiyar tace kamata yayi Igbo su kulla kawance sannan su gina gadar Niger, maimakon haddasa gaba da Musulman arewa

Ana cigaba da yin Allah wadai akan kiran da kungiyar Ohanaeze Ndigbo tayi na cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus saboda ya halarci taron kungiyar kasashen Musulunci (OIC) a kasar Saudiyya.

Buhari ya je kasar Saudiyya washe garin rantsar dashi don halartan taron OIC wanda hakan ya ja hankalin kungiyar Ohanaeze.

A wani jawabin da mataimakin sakataren sadarwar kungiyar na kasa, Chuks Ibegu yayi, ya zargi Buhari da kasancewa mai “tsatstsauran ra’ayin addini”, ya kuma yi kira gare shi da yayi murabus.

Amman shugabancin kungiyar matsan Ohanaeze Ndigbo a fadin duniya tace tayi mamaki da kira ga murabus din shugaban kasa Buhari.

KU KARANTA KUMA: Mazan Kirista su auri mata sama da guda daya, babu ayar Injila da ya haramta hakan - Fasto

Kungiyar tace “sakarci da jahilci ne” yin amfani da sunan kungiyar Igbo wajen yin kiran murabus ga shugaban kasan.

Jawabin ya bayyana cewa lamarin na iya haifar da yakin addinai wanda ka iya canye kasar, musamman yan Igbo dake zama a yankin Arewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel