'Yan bindiga ba su kai min hari ba, samame na kai mafakarsu - Gwamnan Zamfara

'Yan bindiga ba su kai min hari ba, samame na kai mafakarsu - Gwamnan Zamfara

A ranar Lahad ne rahotanni suka bayyana cewar 'yan bindiga sun bude wa tawagar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, wuta a hanyarsa ta zuwa yiwa jama'ar wani gari dake karkashin karamar hukumar Gusau jajen rashi da asarar da suka yi sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai musu.

Amma gwamnan ya ce jami'an tsaronsa ne suka fatattaki 'yan bindiga a wata mafakarsu.

A cewar wwani shaidar gani da ido, 'yan bindigar sun kai harin ne a kan tawagar gwamnan yayinda yake kan hanyarsa ta kauyen Lilo domin yiwa jaje da ta'aziyya.

'Yan bindigar sun yi amfani da yawan ababen hawa dake bin hanyar tare da budewa tawagar gwamnan wuta.

Da gwamnatin jihar Zamfara ke musanta labarin kai wa gwamnan hari a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta ce gwamnan da tawagar jami'an tsaronsa ne suka kai wa 'yan bindigar hari sabanin labarin dake yawo a gari.

'Yan bindiga ba su kai min hari ba, samame na kai mafakarsu - Gwamnan Zamfara

Bello Matawalle - Gwamnan Zamfara
Source: UGC

Yusuf Idris, kakakin gwamna, ya ce Matawalle ne ya jagoranci jami'an tsaro wajen kai wa 'yan bindigar hari a maboyar su.

Idris ya bayyana cewar gwamnan na tare da mataimakinsa, Mahadi Aliyu Gusau, da kuma ragowar shugabannin hukumomin tsaro na jihar Zamfara a lokacin da ya jagoranci kai wa 'yan bindigar hari.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Sabon gwamnan jihar Gombe ya yi sabbin nade-nade 12

A cewarsa, tawagar gwamnan ta samu nasarar fatattakar 'yan bindigar daga sansaninsu a samamen da tawagar ta kai musu.

"Duk da hakan, gwuiwar gwamna ba tayi sanyi ba wajen wuce wa zuwa kauyen Lilo domin yi wa jama'a jaje da ta'aziyya," a cewar jawabin.

Da yake karin haske a kan lamarin, gwana Matawalle ya ce; "a matsayina na babban jami'in tsaron jiha, ya kamata na nuna wa ragowar shugabannin hukomin tsaro da jama'a cewar kyakyawan misali ta hanyar nuna musu yadda na damu na kawo karshen matsalar dake damun jama'a ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel