El-Rufai ya bayyana muhimmin rawar da Buhari ya taka wajen zaben Gbajabiamila

El-Rufai ya bayyana muhimmin rawar da Buhari ya taka wajen zaben Gbajabiamila

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana babbar kalubalen da dan majalisa mai neman kujerar kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yake fuskanta, tare da rawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka wajen kawar da wannan matsalar.

El-Rufai ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakoncin sabbin yan majalisar wakilai da suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin jahar Kaduna a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, inda yace ganin cewa shugaba Buhari da uwar jam’iyyar APC sun yanke shawarar mara ma Gbajabiamila baya, ya zama wajibi a rarrashi Idris Maje Wase.

El-Rufai ya bayyana muhimmin rawar da Buhari ya taka wajen zaben Gbajabiamila

El-Rufai da Gbajabiamila
Source: Twitter

KU KARANTA: Duk abinda zai faru ya faru: Tsohon ministan Jonathan ya kamo danyar dawowa Najeriya

Legit.ng ta ruwaito Wase shine dan majalisa mai wakiltar Wase da Kanam a majalisar dokokin tarayya daga jahar Filato, kuma jigo ne a majalisar kasancewa yan cikin shekara ta 12 kenan a majalisar, kuma yana taimaka ma jama’ansa ta hanyar sama musu ayyukan yi da dama.

“Na fada ma Buhari cewa ya zama dole ka shiga cikin batun zaben shuwagabannin majalisa, ba zaka zauna kana kallonsu ba, don haka idan ka yarda zan saka idanu naga idan akwai wasu kalubale da yan takararka Femi da Lawan zasu fuskanta, sai na sanar dakai kasan matakin da zaka dauka, kuma ya yarda.

El-Rufai ya bayyana muhimmin rawar da Buhari ya taka wajen zaben Gbajabiamila

Wase da Gbajabiamila
Source: Twitter

“Don haka dana tabbatar cewa Wase ne kadai wani babban kalubale da zai iya kawo ma Femi cikas, sai na kirashi don bayyana masa ra’ayin shugaban kasa game da takarar Femi, hakanan na fada ma shugaban kasa akwai bukatar ya rarrashi Wase saboda mai Kaman zuwa zai aika.

“Da wannan ne shugaban kasa ya gayyaci Wase Villa, ya shaida masa cewa ‘Nasan zaka iya zaka iya zama kaakaki, kuma nasan ba lallai kaji dadin matakin dana yanke ba, amma don Allah ka janye ma Femi takarar nan saboda na riga na zabeshi.” Inji shi.

Daga karshe Wase ya kada baki yace ma Buhari “Na san ina da damar zama Kaakaki, amma tunda dai shugaban kasa Buhari yasa baki, na hakura, na janye, saboda ina girmama shugabanni, shine tarbiyyar da aka bani, zan janye ma Femi na kasance mataimakinsa.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel