Sarkin Kano Sanusi ya yanto fursunoni da naira miliyan 5

Sarkin Kano Sanusi ya yanto fursunoni da naira miliyan 5

- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yanto wasu fursunoni gidajen yari na urmawa da Goron Dutse duk a cikin birnin Kano

- Sanusi ya biya tarar da aka ci su har naira miliyan biyar

- Ya shawarce su da suyi amfani da sauran ranakun da ya rage na Ramadana wajen neman gafarar Allah da kuma neman yardarsa domin ya shiga cikin lamarinsu

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya biya naia miliyan biyar na tarar da aka ci wasu fursunoni a gidajen yari na urmawa da Goron Dutse duk a cikin birnin Kano domin neman sakinsu.

Da yake Magana a lokacin ziyarar da ya kai cikin wannan wata na Ramadana, Sarkin ya bukaci fursunonin da su duba zaman da suka yi a ggidan yari a matsayin nufi Allah sannan suyi amfani da hakan wajen koyon darasi.

Ya shawarce su da suyi amfani da sauran ranakun da ya rage na Ramadana wajen neman gafarar Allah da kuma neman yardarsa domin ya shiga cikin lamarinsu.

Ya kuma bukace su da su kasance masu kyawawan halayya domin guje ma duk wani aiki da zai sa su sake komawa gidan yari.

KU KARANTA KUMA: Karamar Sallar: A nemi wata yau - Sarkin Musulmi ya yi umurni

Mukaddashin Shugaban gidajen yari na jihar Kano, Aliyu Yahuza, ya bayyana ziyarar sarkin a matsayin abu da ke nuni ga cewa ya damu da talakawansa.

Ya kara da cewa gidajen yari sun jajirce sosai wajen horar da fursunoni a fannin sana’o’i daban-daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel