An kama mutane 3 kan harin da aka kai gidan Okorocha

An kama mutane 3 kan harin da aka kai gidan Okorocha

Rundunar yan sanda reshen jihar Imo ta kama wasu mutane uku daga cikin wadanda suka kai hari gidan tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha.

An tattaro cewa sun kasance daga cikin ma’aikatan gidan tsohon gwamnan.

Kwamishinan yan sandan jihar, Rabiu Ladodo ya bayyana ma majiyarmu ta jaridar Daily Trust cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa da sain masu aiki a cikin gidan tsohon gwamnan aka kai harin.

Kwamishinan yace: “Mun kama ma’aikatan cikin gidan tsohon gwamnan uku. Bincikenmu ta farko ta bayyana cewa wasu daga cikin ma’aikatan gidan ne suka daukaka harin.

“Ina mai tabbatar ma al’umman Imo cewa mun dauki matakai akan lamarin kuma muna iya kokarinmu don tabbatar da cewa mun kawo karshen lamarin sannan kuma mun cimma adalci”.

KU KARANTA KUMA: Yadda wani Sojan Najeriya ya zamo zakara a jami’ar Ingila

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu yan bindiga da ba a san su wanene ba, wadanda ake zargin hayansu aka yi sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha dake Ogboko, a yankin karamar hukumar Ideato ta kudu a jihar Imo a daren ranar juma’a.

An tattaro cewa yan bindigan sun isa gidan Okorocha da misalin karfe 2 na tsakar dare inda suka ci karfin jami’an tsaron gidan kafin samun damar shiga cikin gidan.

Wani majiya na iyalin, wanda ya nemi a boye sunansa, yace ba a tafi da kaddarori ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel