Oshiomole bai da kwarewar jagorantar babbar jam'iyya irin APC - Tsohon shugaba APC, Oyegun

Oshiomole bai da kwarewar jagorantar babbar jam'iyya irin APC - Tsohon shugaba APC, Oyegun

Tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, John Odigie-Oyegun, ya caccaki salon shugabancin magajinsa, Adams Oshiomole, yayinda ake kira ga murabus dinsa gida da waje.

Game da cewarsa, Oshiomole bai da hakurin jagorantar jam'iyyar siyasa.

Oyegun ya yi wannan jawabi ne matsayin martani ga shugabannin jam'iyyar APC na yankiun kudu maso kudu suka saki na zarginsa cewa shi ke kulla-kullan rikicin da Adams Oshiomole ke fuskanta a yanzu.

A ranar 28 ga watan mayu, mataimakin shugaban jam'iyyar APC, Lawal Shuaibu, ya rubuta budaddiyar wasika inda ya bukaci Oshiomole yayi murabus daga kujerarsa.

Ya bayyana cewa yawancin shawarar da ake alanta cewa kwamitin gudanarwan APC ce ta yi, Adamsa Oshiomole ne kawai ya kakabawa kwamitin ba tare da wani ganawa ko tattaunawa ba.

Amma domin kariya ga Oshiomole, shugabannin jam'iyyar APC na jihohin kudu shiga sun bukaci Lawal shuaibi ya baiwa Oshiomole hakuri kan maganar da yayi, kuma sun daura laifin da John Oyegun.

KU KARANTA: Karamar Sallar: A nemi wata yau - Sarkin Musulmi ya yi umurni

A martaninsa, Oyegun ya siffanta wannan zargi da suke masa matsayin zubar baki da da yarinta kawai.

Ya ce kawai suna kokarin kare rashin kwarewan Oshiomole waje shugabantan jam'iyyar.

Yace: "Oshiomole ya gaza saboda bai da hakurin da aka bukata wajen jagorantar jam'iyyar siyasa. Ba shi da kwarewar gudanar da jama'a da ra'ayoyi daban-daban da akeyi a jam'iyyar siyasa."

"Azarbabinsa ya yi yawa, bai tunani kafin yin magana, saboda haka yana sabawa mambobin jam'iyya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel