Sabon majalisa: Fashola, Hameed, da Adamu suna zawarcin maye gurbin Abba Kyari

Sabon majalisa: Fashola, Hameed, da Adamu suna zawarcin maye gurbin Abba Kyari

- Hasashe sun nuna cewa tsakanin Ritaya Kanal Hameed Ali, Adamu Adamu, Babatunde Raji Fashola wani zai maye gurbin Abba Kyari wajen zama shugaban ma'aikata

- Tuni dai manya jami'an gwamnati da yan siyasa suka fara kamun kafa a wajen abokai da ahlin gidan shugaban kasar domin samun manyan mukamai

- A yanzu dai idanu sun koma kan ganin wadanda za su samu manyan mukaman tarayya kama daga na madafa, majalisar zartarwa da kuma wasu manyan nade-nade

Bayan sauye-sauye da aka samu, alamu sun nuna cewa daya daga cikin mutane uku da suka hada da Ritaya Kanal Hameed Ali, Shugaban hukumar kwastam na Najeriya mai ci, tsohon ministan ilimi, Adamu Adamu, da tsohon gwamnan jihar Lagas kuma ministan ayyuka da ya sauka kwanan nan, Babatunde Raji Fashola na iya zama Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, jaridar Sunday Inependent ta ruwaito.

Bayan antsarwar da aka yi wa Shugaban kasar a makon da ya gabata, wanda shine karo na biyu da Buhari zai shugabancin kasar, idanu sun koma kan ganin wadanda za su samu manyan mukaman tarayya kama daga na madafa, majalisar zartarwa da kuma wasu manyan nade-nade.

KU KARANTA KUMA: Yadda wani Sojan Najeriya ya zamo zakara a jami’ar Ingila

An tattaro cewa mukamin Shugaban ma’aikata da nade-naden ministoci ya zamo abunda mutane da dama ke zawarci, tare da kamun kafa a wajen abokai da ahlin Buhari.

Hakan ya biyo bayan nuna ra’ayin sauye-sauye da Shugaban kasar yayi a shekaru hudu masu zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel