Karamar Sallar: A nemi wata yau - Sarkin Musulmi ya yi umurni

Karamar Sallar: A nemi wata yau - Sarkin Musulmi ya yi umurni

Majalisar koli kan al'amuran addinin Musulunci ta sakin jawabin bada umurnin sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar ga al'ummar Musulmi na neman sabuwar watar Shawwal wanda zai kawo karshen watan Ramadan mai albarka.

Mataimakin sakataren majlisar, Farfesa Salisu Shehu, ya bayyana hakan ne inda ya bada lambobi mambobin kwamitin 30 da duk wanda ya ga watan zai tuntuba.

Jawabi yace: "Bisa ga shawarar kwamitin duban wata ta kasa ga baki daya, shugaban majalisar ya yi kira ga al'ummar Musulmi su nemi sabuwar jinjirin watar Shawwal bayan faduwar ranar yau Litinin, 29 ga watan Ramadana 1440AH wanda yayi dai-dai da 3 ga watan Yuni, 2019.

"Idan Musulmai amintattu suka ga wata da yamma, mai alfarma sarki zai alanta ranar Talata, 4 ga Yuni, 2019 matsayin 1 ga watan Shawwal kuma ranar Sallah."

"Amma idan ba'a ga wata ba, ranar Laraba, 5 ga watan Yni za ta zama ranar 1 ga watan Shawwal 1440 AH kuma ranar Sallah."

"Saboda ahaka ana kira ga Musulmai a fadin tarayya su saurari umurnin da mai alfarma, shugaban majalisar NSCIA kan karshen watan Ramadana."

Hakazalika a kasar Saudiyya, hukumar kasar ta bada umurnin neman watan Shawwal a ranar Litinin. Amma wasu kasashe irinsu Australiya ta rigaya da sanar da cewa ranar Laraba zasu sha bikin karamar Sallah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel