Duk abinda zai faru ya faru: Tsohon ministan Jonathan ya kamo danyar dawowa Najeriya

Duk abinda zai faru ya faru: Tsohon ministan Jonathan ya kamo danyar dawowa Najeriya

Tsohon ministan shari’a a zamanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Mohammed Adoke, wanda ya kwashe shekaru hudu yana buya tare da tserema hukumar EFCC, ya kammala shirin dawoa Najeriya, komai ta fanjama fanjam a cewarsa.

Adoke ya sanar da niyyarsa ta dawowa gida Najeriya ne a wata hira da yayi da jaridar Premium Times, inda yace zai dawo Najeriya a tsakanin watanni Yuli da Satumba domin fuskantar duk ma abinda zai sameshi.

KU KARANTA: Jahohin Najeriya 36 da adadin makudan basussukan dake kan kowannensu

Duk abinda zai faru ya faru: Tsohon ministan Jonathan ya kamo danyar dawowa Najeriya

Adoke
Source: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar EFCC ta dade tana farautar Adoke da nufin jin bahasin rawar daya taka wajen badakalar cefanar da rijiyar danyen man fetir na Malabu akan dalan amurka biliyan 1, fiye da naira biliyan 360 kenan.

Amma a bangare guda kuma Adoke ya sha musanta wadannan zarge zarge, wanda hakan yasa wata kotu a karkashin jagoran Mai Sharia Binta Nyako ta wankeshi daga tuhume tuhumen da ake yi masa, inda tace bai aikata wani lafi ba.

Adoke yace ya bar Najeriya ne da nufin kara karatu a birgin Hague, amma daga bisani ya samu labarin ana nemansa ruwa a jallo a Najeriya, hakanan ya tsaya an duba lafiyarsa a kasar waje, sa’annan har ya fara rubuta littafinsa kan rawar daya taka a mukaminsa na Minista.

Daga karshe Adoke ya bayyana Najeriya a matsayin wata kasa mai wuyar sha’ani, kasar da bata godiya ga wadanda suka yi mata bauta, suka sha wuyarta, inda yace duk da irin kokarin da yayi ma Najeriya, amma abinda za’a saka masa dashi kenan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel