Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halaratar taron OIC a saudiyya (Hotuna)

Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halaratar taron OIC a saudiyya (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan kammala taron kungiyar hadin kan kasashen Muslmi (OIC) karo na 14 da aka yi a kasar Saudiyya.

Da yake sanar da dawowar shugaba Buhari a shafinsa na Tuwita, mai taimakawa shugaban kasa a bangaren kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya bayyana cewar Buhari ya nuna jin dadinsa bisa yadda kasashen kungiyar OIC suka nuna niyyar bayar da tallafi ga aikin farfado tafkin tekun Chadi.

Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halaratar taron OIC a saudiyya (Hotuna)

Dawowar Buhari
Source: Twitter

Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halaratar taron OIC a saudiyya (Hotuna)

Buhari na saukowa daga jirgi
Source: Twitter

Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halaratar taron OIC a saudiyya (Hotuna)

Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halaratar taron OIC
Source: Twitter

Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halaratar taron OIC a saudiyya (Hotuna)

Buhari ya dawo gida Najeriya
Source: Twitter

Kafin ya baro kasar Saudiyya, Legit.ng ta kawo muku labarin cewar Tsohon shugabar kasar Najeriya a mulki soji, Abdulsalamu Abubakar, ya ziyarci shugaba Buhari a kasar Saudiyya domin gana wa ta musamman. Babu wata sanarwa ko bayani a kan dalilin ganawar shugabannnin biyu a kasar Saudiyya. Shugaba yana kasar Saudiyya ne domin halartar taron kasashen Musulmi na OIC.

DUBA WANNAN: Gidauniyar Sheikh Gumi ta bawa Kwankwaso kyautar iya jagoranci

Tuni sanarwa ta fita cewar shugaba Buhari zai karbi bakuncin shugabannin kasashen gefen tekun Chadi kwanaki kadan bayan dawowarsa daga kasar Saudiyya. Ana tunanin taron ba zai rasa nabasa da gudunmawar da kungiyar kasashen OIC zata bayar ba wajen farfado da tekun Chadi.

A kwanakin baya ne babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antoni Guterres, ya nada shugaba Buhari a matsayin wanda zai zama shugaba na biyu a kwamitin neman hada kudaden da za ai amfani da su domin farfado da tekun Chadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel