Rayuka 35 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 6 cikin Najeriya a makon da ya gabata

Rayuka 35 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 6 cikin Najeriya a makon da ya gabata

Babu sauki al'amari na rashin tsaro ya kai intaha yayin da ta'addanci ke ci gaba da ta'azzara a fadin kasar nan inda a makon da ya gabata kadai rayukan al'ummar Najeriya 35 suka salwanta yayin aukuwar wasu munanan hare hare.

A makon da ya gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya danganta annobar rashin tsaro a fadin Najeriya da gazawar hukumar 'yan sanda da kuma rundunar dakarun tsaro ta soji a yayin da shugaban hafsin sojin kasan Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi ikirarin cewa an ci galaba akan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, a yayin da kasar nan ta yi tsamo tsamo cikin wannan yanayi na zargi tare da dora laifin tabarbarewar tsaro a Najeriya, da yawa daga cikin al'ummar kasar na ci gaba da afkawa tarkon miyagun 'yan ta'adda.

Shakka babu a makon da ya gabata kadai al'ummar Najeriya kimanin 35 sun riga mu gidan gaskiya yayin da mutane shida suka afka taron miyagun 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa.

KARANTA KUMA: Da karfin tsiya zan magance Boko Haram a Najeriya - Buhari

Cikin jihohin da lamari na ta'addancin masu garkuwa da mutane, Boko Haram da kuma rikici a tsakanin al'umma ya auku a fadin a kasar nan cikin makon da ya gabata kacal sun hadar da Filato, Bayelsa, Zamfara, Benuwai, Katsina da kuma Borno.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel