Ba zan yi gaggawar nadin mukamai ba - Gwamnan Nasarawa

Ba zan yi gaggawar nadin mukamai ba - Gwamnan Nasarawa

Sabon gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Alhaji Sule, ya yi karin haske da cewar ba ya da nufin yin aikin gaggawa wajen nadin mukamai na hadimai a sabuwar majalisar gwamnatin sa yayin da ya karbi akalar jagoranci.

Injiniya Abdullahi ya yi wannan furuci yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Lahadi cikin birnin Lafiya. Ya ce ba zai yi aikin gaggawa ba wajen nadin kwamishinoni domin gudun afkawa ramin kurakurai.

A halin yanzu sabon gwamnan na jihar Nasarawa na ci gaba da gudanar da nazari na fahimtar yadda tsohuwar gwamnatin jihar ta aiwatar da salon mulkin ta wajen riko da akalar jagoranci kamar yadda ya shaidawa manema labarai.

Gwamnan ya ce tuni ya fara tuntube tuntube tare da ganawa da manyan sakatarorin gwamnatin jihar da kuma shugabannin kananan hukumomi da na hukumomin tsaro domin tumke damarar sa ta bayar da muhimmanci wajen ingancin tsaro a jihar.

KARANTA KUMA: Da karfin tsiya zan magance Boko Haram a Najeriya - Buhari

A yayin da ya shiga fadar gwamnatin jihar a ranar Alhamis bayan karbar rantsuwa a ranar Laraba 29 ga watan Mayun 2019, gwamna Abdullahi ya gargadi al'ummar jihar Nasarawa a kan muhimmancin wanzar da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel