Da karfin tsiya zan magance Boko Haram a Najeriya - Buhari

Da karfin tsiya zan magance Boko Haram a Najeriya - Buhari

Bayan kammala babban zaben kasa na 2019 inda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi nasara a karo na biyu, kasar Najeriya ba ta gushe ba wajen ci gaba da fuskantar kalubale na ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Shakka ba bu matsalar ci ga da aukuwar hare-haren kungiyar Boko Haram mai alaka da mafi munin kungiyar ta'adda a doron kasa ta ISIS, na daya daga cikin manyan kalubale da ke kan sahu na gaba a zango na biyu na mulkin Buhari.

A halin yanzu shugaban kasa Buhari zai kasance mai masaukin baki yayin taron shugabannin kungiyar kasashen gabar tafkin Chadi, Lake Chad Basin Commission, da za a gudanar yayin bikin rantsuwar sa na 12 ga watan Yunin 2019, a garin Abuja.

Taron kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu ya bayyana, zai bayar da mafificin muhimmanci na shimfida matakan kawo karshen annobar ta'addancin Boko Haram a yankunan gabar tafkin Chadi.

Da yake ganawa da shugaban kasar Chadi, Idris Deby Itno, yayin halartar taron kungiyar kasashen hadin kan musulmi na duniya a kasar Saudiya, shugaba Buhari ya ce lokaci ya karato da ya kamata a kawo karshen ta'addanci ta karfin tsiya a yankunan gabar tafkin Chadi.

KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta gargadi shugabannin tsaro akan tsare rayukan al'ummar Najeriya

Shugaban kasa Buhari ya ce tun da a yanzu kakar zabe ta yanke a Najeriya, zai karkatar da akalar sa ta bayar da fifikon muhimmanci wajen tunkarar ta'addancin kungiyar Boko Haram da karfin tsiya.

Buhari da kuma takwaransa na kasar Chadi sun tattauna a kan batutuwan kalubale musamman a wannan lokaci na damina da dakarun soji ke fuskanta a yayin yakar ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel