Malamin Islama ya bukaci Buhari gaggauta sakin Dasuki da El-Zakzaky

Malamin Islama ya bukaci Buhari gaggauta sakin Dasuki da El-Zakzaky

Ftaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki Sambo Dasuki, tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Goodluck Jonathan, ba tare da wani bata lokaci ba.

Kazalika, Malamin ya yi wani kira ga gwamnatin a kan ta saki shugaban mabiya kungiyar shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Sheikh Gumi ya yi wannan kira ne ranar Asabar yayin rufe karatun tafsirin watan azumin Ramadana a masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna. Ya ce akwai bukatar gwamnati take yi wa umarnin biyayya.

Gumi ya kara da cewa babu dalilin cigaba da tsare mutanen biyu tunda tuni ta bayar umarnin a sake su.

Malamin Islama ya bukaci Buhari gaggauta sakin Dasuki da El-Zakzaky

Sheikh Gumi
Source: Depositphotos

Ya ce zai fi sauki ga gwamnatin tarayya ta yi sulhu da Sheikh Zakzaky a kan cigaba da tsare shi a kurkuku.

"A nan gida Najeriya, ina son yin kira ga gwamnati da ta kara duba lamarin Kanal Sambo Dasuki domin a sako shi ba tare da bata lokaci ba, haka ma shugaban 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

DUBA WANNAN: Sabon gwamnan Zamfara ya sadaukar da albashinsa ga gidan marayu

"Su sake shi idan ya so sai su tattauna da shi domin su fuskanci juna. Ba daidai bane gwamnatin ta ki yin biyayya ga umarnin kotu.

"Matukar gwamnati ba ta yi biyayya ga doka ba, dole a samu haramtattun kungiyoyi da zasu ke taka doka da gangan. Babu wani uzurin aikata ta'addanci.

"Dole gwamnati ta nuna kyakyawan misali ta hanyar sakin su, musamman kanal Sambo Dasuki," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel