Ministoci da za su dawo a sabuwar Majalisar Buhari

Ministoci da za su dawo a sabuwar Majalisar Buhari

Kawo wa yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai fayyace jerin Ministoci da zai nada a sabuwar gwamnatin sa ba cikin wa'adin ta na biyu domin ci gaba da rike madafan iko wajen karkartar da akalar jagoranci a ma'aikatu daban daban.

Duk da kasancewar wannan lamari akwai yiwuwar shugaban kasar zai sake yiwa wasu daga cikin tsaffin ministocin sa nadin mukamai a sabuwar majalisar gwamnatin sa cikin wa'adin ta a karo na biyu.

Ana tuna cewa shugaba Buhari a ranar Litinin ta makon da ya gabata yayi karin haske da cewar zai ci gaba da rike wasu daga cikin Ministocin sa a sabuwar gwamnatin sa yayin da wa'adin sa na farko a karagar mulki ya kawo karshe.

Furucin shugaba Buhari ya zo ne yayin wata sanarwa da ya gabatar a jajibirin ranar karbar rantsuwa inda ya nemi ministocin sa da su yi zube ban kwarya tare da bajakolin kwazon da suka yi yayin sauke nauyin da rataya masu na ma'aikatu daban daban.

Binciken da manema labarai na jaridar Leadership suka gudanar ya bayyana cewa, akwai jerin wasu ministocin shugaban kasa Buhari da zasu koma cikin sabuwar majalisar sa biyo bayan kwazon aiki da hausawa ke cewa don tuwon gobe ake wanke tukunya.

Babu lallai wadannan ministoci su dawo cikin sabuwar majalisar wajen ci gaba da rike jagorancin tsaffin ma'aikatun su. Jerin tsaffin ministocin sun hadar da ministan sufuri Chibuike Amaechi, ministan ilimi Adamu Adamu, ministan noma Aude Ogbe, karamin ministan jiragen sama Hadi Sirika da kuma ministan ruwa, Suleiman Adamu.

KARANTA KUMA: Tsohon Ministan Sadarwa ya nemi Oshiomhole ya yi murabus

Sauran tsaffin ministocin da ake sa ran dawowar su a sabuwar majalisar sun hadar da ministan kasafi da tsare tsaren kasa Udoma Udo Udoma, ministan makamashi, ayyuka da kuma gidaje Babatunde Fashola, ministan labarai da al'adu Lai Muhammad, ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau, ministan shari'a Abubakar Malami, karamar ministan masana'antu da hannun jari, Aisha Abubakar, da kuma ministan zamantakewa Suleiman Hassan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel