Jerin sunaye: El-Rufa'a ya yi sabbin nade-nade guda biyar

Jerin sunaye: El-Rufa'a ya yi sabbin nade-nade guda biyar

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya sake Samuel Aruwan, a matsayin mai magana da yawunsa a karo na biyu.

Tun bayan bikin rantsuwa sabbin zababbun gwamnoni suka fara bayar da wasu daga mukaman siyasa a jihohinsu.

Aruwan, wanda tuni sunansa ya zama sananne a jihar Kaduna da kewaye, ya kasance kakakin gwamna El-Rufa'i a zangon mulkinsa na farko.

Labarin nadin Aruwan tare da ragowar mutanen, na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Salisu Suleiman, sakataren gwana El-Rufa'i, ya fitar da yammacin ranar Asabar.

Jerin sunaye: El-Rufa'a ya yi sabbin nade-nade guda biyar

Malam Nasir El-Rufa'i
Source: Depositphotos

Ga sunayen wadanda aka nada tare da Aruwan:

1 – Maryam Abubakar, Babban mai taimakawa wa gwamnan El-Rufai kan sabbin kafafen yada Labarai.

DUBA WANNAN: Sabon gwamnan Zamfara ya sadaukar da albashinsa ga gidan marayu

2 – Saude Amina Atoyebi, Babban mai taimakawa gwamnan a kan Ayyuka.

3. Mukhtar Maigamo​​, Mai taimakawa wa gwamna a bangaren hulda da jama’a

4. Manasseh Istifanu, Mai taimakawa gwamna a kan harkokin yada Labarai.

4. Nuhu John Gwamna, mai daukan hoto na musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel