Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai wa Rochas Okorocha hari har gida

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai wa Rochas Okorocha hari har gida

Wasu yan bindiga da ba a san su wanene ba, wadanda ake zargin hayansu aka yi sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha dake Ogboko, a yankin karamar hukumar Ideato ta kudu a jihar Imo a daren ranar juma’a.

An tattaro cewa yan bindigan sun isa gidan Okorocha da misalin karfe 2 na tsakar dare inda suka ci karfin jami’an tsaron gidan kafin samun damar shiga cikin gidan.

Wani majiya na iyalin, wanda ya nemi a boye sunansa, yace ba a tafi da kaddarori ba.

Yan bindigan sun binciki dakin tsohon gwamnan, wanda wannan ne yasa ake zatton hayansu aka yi.

An tattaro cewa wata kungiyar yan bindiga, wadanda ake zargin jami’an gwamnati ne, sun kai hari gidan radiyon Reach FM, na gwamnan inda suka yi umurnin cewa a rusa ginin inda gidan radiyon ke kafe.

Daya daga cikin jami’an tsaron gidan radiyon ya fada ma majiyarmu ta Daily Trust cewa yan bindigan sun ki bayyana asalinsu, amman sun baiwa manyan ma’aikatan wa’adin kwana uku su rusa ginin ko kuma a rusa ta karfi da yaji.

KU KARANTA KUMA: Kayi gaggawar sakin Dasuki da El-Zakzaky - Sheikh Gumi ya gargadi Buhari

Lamarin ya auku ne sa’o’i 48 bayan an rusa sanannen Akachi tower, daya daga cikin abun tunawan da tsohon gwamnan ya gina, wanda ake zatton gwamnatin jiha ne ta bada umurnin.

Haka zalika, a lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundanar sanda na jihar, Orlando Ikeokwu, ya bayyana cewa bai samu jawabai ba tukun akan harin da aka kai gidan tsahon gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel