Aisha Buhari ta aika muhimmin sako ga shugabanin hukumomin tsaro

Aisha Buhari ta aika muhimmin sako ga shugabanin hukumomin tsaro

Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta kallubalanci hukumomin tsaro suyi gaggawan kawo karshen hare-haren 'yan bindiga da sauran kallubalen tsaro da ake fama da su a sassan kasar.

Aisha tayi wannan kirar ne a ranar Asabar yayin da ta ke bayar da tallafi kayayaki ga mutane fiye da 25,000 da harin 'yan bindiga ya ritsa da su inda ta ce ya zama dole a magance 'yan bindigan kafin su gama kashe al'umma.

"Ko hukumomin tsaro su taimaka wajen daukan mataki a kan lamarin ko kuma su bari lamarin ya cigaba da tabarbarewa har lokacin da 'yan bindigan za su kammala kashe mutanen mu," inji ta.

Uwar gidan shugaban kasar ta ce dukkan masu son cigaban Najeriya su tashi tsaye suyi magana kan matsalolin da ke adabar kasar domin a dauki matakan da suka dace.

DUBA WANNAN: Yadda wata mata ta yi wa kanta tiyata da reza ta ciro jariri

"Bai dace mu zo nan muna raba shinkafa da madara da sauran kayayaki ga al'ummar da harin ya ritsa da su ba cikin watan Ramadana.

"Ba dace muyi shiru bu yayin da abubuwa ke cigaba da faruwa muna tunanin cewa ba za su cigaba da faruwa ba.

"Abinda ya faru yau zai faru gobe, zai faru jibi muddin mu ka cigaba da yin shiru.

"Ya zama dole mu fadi gaskiya, ba dace mutane su bamu kuri'u yayin zabe ba amma mu bari 'yan bindiga su cigaba da kashe su kuma muyi shiru.

"Dole muyi magana a kan duk wani abu da bai dace ba a kasar nan," inji ta.

Aisha Buhari ta ce ita da matan tsafin gwamnonin Nasarawa da Bayelsa da Adamawa da Akwa Ibom (Godswill Akpabio) suna daga cikin wadanda suka bayar da tallafin kayayaki ga wadanda rikicin ya shafa.

Da farko, Hakimin Katsina, Aminu Abdulmumini ya mika godiyarsa da matar shugaban kasar bisa tallafin da ta bayar.

Ya yi kira da gwamnati ta kara dagewa wurin ganin an kawo karshen hare-haren na 'yan bindigan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel