Dalilin da yasa Sokoto ke fuskantar karancin ruwa – Tsohon kwamishina

Dalilin da yasa Sokoto ke fuskantar karancin ruwa – Tsohon kwamishina

Rashin tsare tsare da kula suna daga cikin manyan matsalolin da ya haifar da rashin samun isasshen ruwa a Sokoto.

“Ana ta samun kari a yawan al’umma amman babu wanda ke tsara abubuwa. A halin yanzu hukumar samar da ruwa a jihar Sokoto na da inganci, matsalar kawai shine mun ki ba mashinan kulawa” inji tsohon Kwamishinan ruwa Alhaji Umar Muhammad Bature.

Ya kara da cewa: “Tsarin samar da ruwa ya kasance a kasa tun 1988, akalla shekaru 31, saboda an samu ‘karuwa kuma hakan yasa layin bututu bai kai wasu yankuna ba, wannan ne sababin rashin samun ruwa a wadannan yankunan."

Bature yace a lokacin da ya kama aiki a matsayin kwamishinan ruwa a Watan Nuwamba, ya zo da tsare-tsare na aiki.

“Tsari na farko da nazo da shi ya hada da gyare-gyaren mashina. Na biyu shine inganta tsarin samar da ruwa sannan tsari na uku ya kasance a samar da isasshen ruwa.”

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yi umurnin tsare matar da tace macijiya ta hadiye N35m na JAMB

Ya bayyana cewa: “mun samar da damar samun ruwa daga kashi 0 zuwa kashi 60.

"A bangaren samar da ruwa, mun gyara hudu daga cikin fonfuna shida, kuma muna kokari don ganin mun gyara sauran fonfuna biyun.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel