Kotu ta yi umurnin tsare matar da tace macijiya ta hadiye N35m na JAMB

Kotu ta yi umurnin tsare matar da tace macijiya ta hadiye N35m na JAMB

Wata babbar kotun Abuja da ke Maitama a jiya, Juma’a, 31 ga watan Mayu ta tsare wata mata mai suna Philomina Chieshe da wasu jami’an hukumar JAMB guda biyar da ke da hannu a batan naira miliyan 35 daga kudin cibiyar JAMB a jihar Benue.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sun yi zargin cewa Chieshe, ma’aikaciyar hukumar, ta fada ma wani kwamitin bincike cewa ta kasa bayar da bayani akan cinikin da tayi a shekarun baya kafin hukumar ta dakatar da siyar da katuna.

An tattaro cewa tayi ikirarin cewa wata macijiya ce ta hadiye kudin a Makurdi, babbar birnin jihar.

Chieshe ta fada ma kwamitin cewa yar aikinta ta hada kai da wani jami’in JAMB, domin suyi asiri da macijiya, sannan suka sace kudin daga ofishin akawu.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: An gurfanar da ma'akaciyar JAMB da tace Macijiya ta hadiye miliyan 36 (Hotuna)

An gurfanar da ita a jiya Juma’a tare da Samuel Umoru, Yakubu Jekada, Daniel Agbo, Priscilla Ogunsola da kuma Aliyu Yakubu akan tuhume-tuhume takwas da suka hada da kin ba da bayani akan kudin hukumar tsakanin 2014 da 2016. Sai dai sun ki amsa laifin.

Justis Peter Afen yayi umurnin tsare su a hannun EFCC, sannan ya dage Shari’an zuwa ranar 3 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel