Wasu fusatattun dalibai sun kone asibitin jami'a a jihar Osun, saboda mutuwar wani dalibi

Wasu fusatattun dalibai sun kone asibitin jami'a a jihar Osun, saboda mutuwar wani dalibi

- Wasu fusatattun dalibai sun kone asibitin kwalejin Polytechnic na jihar Osun

- Daliban su n kone asibitin ne saboda mutuwar wani dalibi, inda suke zargin ya mutu saboda rashin samun kulawa

A yau Asabar dinnan ne daliban kwalejin Polytechnic ta jihar Osun, suka sanyawa gurin karbar magani na makarantar wuta akan mutuwar wani dalibi a makarantar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana rahoton cewa masu gadin kwalejin ne suka yi kokarin hana wutar yaduwa zuwa wasu wuraren, inda suka samu suka kashe ta cikin gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa, wani dalibi mai suna Aminu Hammed, wanda yake karatun difloma a bangaren kimiyya, ya fadi a dakin jarrabawa jiya Juma'a inda aka yi kokarin garzayawa dashi zuwa asibitin makarantar, inda daga baya ya ce ga garinku nan.

Wasu fusatattun dalibai sun kone asibitin jami'a a jihar Osun, saboda mutuwar wani dalibi

Wasu fusatattun dalibai sun kone asibitin jami'a a jihar Osun, saboda mutuwar wani dalibi
Source: UGC

Daliban da suka fara zanga-zangar yau Asabar dinnan da safe, sunyi zargin cewa babu ma'aikata a asibitin lokacin da aka kai Hammed da zasu ceto rayuwarsa.

A lokacin zanga-zangar, daliban sun sanyawa motar asibitin wuta, sun kone magunguna da kayyaki da yawa a asibitin.

KU KARANTA: Jerin gwamnonin da suka shafe fiye da shekaru takwas akan mulki

Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na makarantar, Mista Tope Abiola, ya ce bayan kone asibitin, akwai kaya na miliyoyin nairori da daliban suka kone.

Ya ce, karya ne zargin da daliban suke yi na cewa babu ma'aikata a asibitin da zasu lura da Hammed lokacin da aka kai shi asibitin.

Abiola ya ce lokacin da aka kai Hammed asibitin da misalin karfe 4:30 na yamma, ma'aikatan asibitin sunyi iya bakin kokarinsu wurin ganin sun ceto rayuwarsa amma a banza.

Ya ce sun aika da Hammed zuwa wani asibiti a cikin garin, inda daga baya ce ga garinku nan.

Abiola ya ce domin kawo karshen zanga-zangar daliban, makarantar ta bada sanarwar rufe makarantar cikin gaggawa.

Ya ce an umarci duka daliban su fita daga makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel