Boko Haram tayi wa wani mutum yankan rago a masallacin Borno

Boko Haram tayi wa wani mutum yankan rago a masallacin Borno

-Kungiyar Boko Haram ta tafka wani mummunan ta'adi a masallacin Sajeri dake jihar Borno.

-Yan kungiyar ta Boko Haram sun kai hari masallacin ne yayin da ake sallar tahajjud inda suka kama wani mutum su kayi mashi yankan rago a baina jama'a.

Yan kungiyar Boko Haram dauke da muggan makamai sun kai farmaki masallacin Sajeri a daren jiya inda suka yanka mutum guda.

Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa ya ce yan ta’addan sun zo garin Sajeri cikin dare a daidai lokacin da ake sallar Tahajjud a masallaci.

KU DUBA WANNAN:Yaki da ta’addanci: NAF ta yaye dalibai 51 bayan samun horo na musamman

Duk da cewa babu cikakken bayani akan aukuwar lamarin, wata majiya mai karfi ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa yan ta’adda sun shiga garin ne inda suka buda wuta akan ma su yin sallar tahajjud.

Tuni jama’a suka kidime kowa yana neman inda zai je domin ya tsira. Hakan ya sanya mutane da dama sun samu mumunan raunuka a sakamakon guje-gujen da suka yi.

“ Yan ta’addan sun damke wani mutum kuma suka yi mashi yankan rago shi a fili, yayin da da dama daga cikin masu sallar ke gudu suna kokarin shiga Ngomari,” inji wata majiya mai tushe wacce ta ba Daily Trust labari.

“Har yanzu babu daya daga cikin wadanda suka jikkata da aka samu kaiwa asibiti, sai dai wasu daga cikinsu na gida suna karbar dan taimakon da ba a rasa ba.” Kamar yadda wata majiyar ta tabbatar mana.

Har ila yau babu wani zance daga hukumomin tsaro a kan aukuwar wannan abu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel