Ohanaeze ta cacaki Buhari saboda hallartar taron OIC a Saudiyya

Ohanaeze ta cacaki Buhari saboda hallartar taron OIC a Saudiyya

Kungiyar 'Yan kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo ta cacaki Shugaba Muhammadu Buhari saboda halartar taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulunci a Saudiyya sa'o'i 24 bayan rantsuwar kama aiki zango na biyu.

A sanarwar da Mataimakin Sakataren Yada Labarai na kungiyar ya fitar, ya ce 'yan Najeriya suna bukatar bayani daga Buhari.

Ohanaeze ya ce, "Mene zai sa ya tafi taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulunci a Saudiyya kwana daya bayan yin rantsuwar kama aiki zango na biyu. Ya kamata shugaban kasa ya yiwa 'yan Najeriya bayani."

DUBA WANNAN: Zanga-zanga: Jami'an tsaro sun shiga farautar mabiya Shi'a a Abuja

Ohanaeze ta kuma ce, "Najeriya ba kasa ce da ake mulki da dokokin addini ba kuma duk shugaban da ya ke sha'awar zama mullah ko mai tsatsauran ra'ayi yana iya yin murabus a maimakon jefa mu cikin rikicin addini."

Kungiyar ta kuma soki shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila saboda tafiya Umrah a kasar Saudiyya.

Sanarwar ta ce, "Femi Gbajabiamila haifafen Kirista ne amma daga bisani ya zama musulmi saboda dalilan siyasa kuma hakan yana da hatsari ga demokradiyyar mu.

"Duk da cewa kowa yana da ikon canja addininsa, yadda ya canja daga Kirista zuwa Musulmi cikin gaggawa sannan ziyarar da ya kai Makkah ba abin alheri bane.

"Shin za mu iya yarda da mutumin da zai iya canja addininsa saboda neman mukami?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel