Tanzania ta haramta amfani da leda

Tanzania ta haramta amfani da leda

-Kasar Tanzania ta shiga jerin kasashen Afrika da suka hana amfani da leda a fadin nahiyar tasu.

-Wannan dokar hana amfani da leda a kasar Tanzania na dauke da tarar dala 90 ko kuma dauri a gidan kaso na tsawon mako guda ga duk wanda ya keta ta.

Tanzania ta zamo kasa ta 34 a nahiyar Afrika da ta haramta amfani da leda a duk fadin kasar. Duk wanda aka samu na saidawa ko amfani da leda domin nade kaya a shaguna ko kasuwa zai biya tarar $90 kimanin N32,400 ko kuma daurin mako guda a gidan kaso.

A bangaren kamfanonin dake samar da ledodin kuwa tara ce ta dubban daloli da daurin kusan shekara biyu a gidan yari.

Tanzania ta haramta amfani da leda

Tanzania ta haramta amfani da leda
Source: Twitter

KARANTA WANNAN:‘Yan sanda sun kama mutum 12 da ake zargi da laifin fashi da kuma garkuwa da mutane a Jigawa

Haramcin ya shafi har matafiya dake shigowa kasar inda tun a filin saukar jiragen sama da tashoshin mota za a umarci jami’an tsaro da su binciki kayayyakinsu ciki har da jakar hannu ta mata.

Har wa yau, wannan matakin da Tanzania ta dauka mai sauki ne idan aka kwatanta da tsattsauran hukuncin da makwabciyarta wato Kenya ta sanya akan duk wanda ya karya dokar.

Jami’an kula da muhalli na MDD sun ce yawancin kasashen da suka dauki matakin haramta amfani da leda, sun gagara samar da jakunkunan kwali ko yadi da ‘yan kasar za suyi amfani da su hakan ya sanya jama’a cikin matsatsi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel