Daukar aikin NNPC: Yadda tsarin ya faro tun farko da kuma korafin jama’a akansa

Daukar aikin NNPC: Yadda tsarin ya faro tun farko da kuma korafin jama’a akansa

Hukumar kula da matatar mai ta kasa wato NNPC ta fitar da sanarwa kan daukar sabbin ma’aikata a shafinta na yanar gizo da kuma jaridu a ranar Laraba 13 ga watan Maris, 2019 wanda a halin yanzu aka iso zuwa matakin rubuta jarabawa.

Kashi na biyu cikin tsare-tsaren hukumar domin tantance wadanda suka fi dacewa da ma’aikatar tasu ya fara ranar 27 ga watan Maris, 2019, inda aka fitar da sunayen wadanda suka cika sharadin hukumar domin rubuta jarabawa a yau Asabar 1 ga watan Yuni, 2019.

KU KARANTA:‘Yan sanda sun kama mutum 12 da ake zargi da laifin fashi da kuma garkuwa da mutane a Jigawa

“ Mun aika da sako ta kafar sada zumunta ta email da kuma rubutaccen sako zuwa lambobin wayar wadanda suka yi nasarar zuwa mataki na gaban.” Inji hukumar.

Jarabawar ta CBT ta gudana a cibiyoyi 50 dake fadin kasar nan,inda zata taimaka wajen tace mutane mafi dacewa kana kuma daga bisani sai a kira su zuwa mataki na karshe.

Jaridar Daily Trust ta samu zantawa da wasu daga cikin wadanda suka nemi gurbin wannan aiki. Ga abinda dayansu mai suna Osaheni Pius-Usiobaifo yake cewa, “ Nayi bakin cikin rashin kira na jarabawar nan da ba’a yi ba. Ina da digiri har biyu wato Masters.” A cewarsa.

Ita kuwa wata mata mai suna Maryam Abdullahi cewa tayi ta tabbata wadanda suka cancanta sune aka kira zuwa wurin jarbawar. “ NNPC ba karamar ma’aikata bace don haka idan ban samu ba nasan cewa cancanta ce ban yi. Akwai kwararru a ma’aikatar sosai, kuma na dade ina son naga na samu aiki da su.” Inji Maryam.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel