Yaki da ta’addanci: NAF ta yaye dalibai 51 bayan samun horo na musamman

Yaki da ta’addanci: NAF ta yaye dalibai 51 bayan samun horo na musamman

-NAF ta yaye jami'ai 51 bayan sun samu horo na musamman a gida Najeriya.

-A halin yanzu dai daliban da suka samun irin wannan horon sun karu zuwa mutane 95, wannan horon na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron Najeriya ke kokarin yaki da ta'addanci.

Rundunar sojin saman Najeriya wato NAF ta yaye dalibai 51 wadanda suka samu horo a ciki gida a ‘Course2/2019’, wanda ya kara yawan jami’an da suka samu irin wannan horon zuwa 95.

Wannan horon ya kasance daya daga cikin kudurin NAF na samar da wadatattun jami’ai domin shawo kan matsalar tsaro dake addabar kasar nan.

Yaki da ta’addanci: Rundunar sojin saman Najeriya ta yaye jami’ai 51 bayan samun horo na musamman

Yaki da ta’addanci: Rundunar sojin saman Najeriya ta yaye jami’ai 51 bayan samun horo na musamman
Source: Facebook

KU KARANTA:‘Yan sanda sun kama mutum 12 da ake zargi da laifin fashi da kuma garkuwa da mutane a Jigawa

Jami’in hulda da jama’ar rundunar Komodo Ibikunle Dara Daramola ya bayyana cewa wannan tsarin horon ya biyo bayan umarnin babban Hafsin sojin saman Najeriya Sadik Abubakar domin a magance matsalolin tsaron kasar nan.

Anyi bikin yaye jami’an ne a cibiyar koyar da harbi ta rundanar dake Kaduna. Daga cikin abubuwan da daliban da aka yaye sukayi akwai fareti da kuma atisaye irin nasu na sojoji.

Da yake magana wurin bikin, hafsun sojin saman, Abubakar ya nuna farin ciki bisa abinda idonsa ya gane masa daga wurin daliban da aka yaye.

Ya kara da cewa, a shekarun baya NAF na samun irin wannan horon ne a kasar Israila amma sai ga shi a yanzu mun iya bayar da horon da kanmu a nan gida.

Bugu da kari, NAF zata bude cibiyoyi a jihohin Osun, Owerri da kuma Bauchi domin karfafa bayar da irin wannan horon ga jami’anta.

Kazalika, bai manta da jami’an NAF dake fagen daga a yankin arewacin kasar nan inda ya kunshi jihohin; Zamfara, Binuwe, Kaduna, Taraba, da kuma hanyar dake tsakanin Abuja zuwa Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel