'Yan Boko Haram sun yi awon gaba da mutane 13 a wani kauye

'Yan Boko Haram sun yi awon gaba da mutane 13 a wani kauye

- A wasu rahotanni da muka samu ya nuna cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sunyi awon gaba da mutane 13 a wani kauye na jamhuriyar Nijar

- A cikin mutanen da 'yan bindigar suka sace akwai matan aure guda uku da kuma wani malami da suka kashe

A rahotannin da muka samu daga jihar Diffa ta jamhuriyar Nijar wacce ke makwabtaka da jihar Borno da Yobe, ya tabbatar da kai hari da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka yi, inda suka sace mutane 13.

Lamarin ya afku a garin Timur, wanda ke da nisan kimanin kilomita 60 zuwa jihar Diffa.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa, wanda ya nemi a boye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewa, cikin daren Laraba wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari garin Timur inda suka yi awon gaba da mutane 13 a garin.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An kashe mutane 6, an kuma raunata 4 a wani hari da 'yan bindiga suka kai kan kabilar Jukun

Mutumin ya kara da cewa, a cikin mutanen da 'yan bindigar suka sace akwai matan aure guda da kuma wani babban malami da aka kashe.

Mutumin ya bayyana cewaa har ya zuwa yanzu ba a sake jin duriyar mutanen da aka sace din ba.

Mutumin ya koka, inda yake cewa "Gaskiya muna cikin zaman dar-dar a gidajenmu, saboda mutum zai kwanta da dare ba tare da tabbacin ko zai tashi ko ba zai tashi ba."

Ya kara da cewa duk da irin kokarin da jami'an tsaro ke yi a yankunan nasu, har yanzu akwai matsalar tsaro a bangaren su.

Har yanzu dai mahukunta a kasar basu yi wata magana ba game da sace mutanen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel