Yanzu-yanzu: An kashe mutane 6, an kuma raunata 4 a wani hari da 'yan bindiga suka kai kan kabilar Jukun

Yanzu-yanzu: An kashe mutane 6, an kuma raunata 4 a wani hari da 'yan bindiga suka kai kan kabilar Jukun

- Wani hari da 'yan bindiga suka kai wani kauye a jihar Taraba yayi sanadiyyar mutuwar mutane 6, sanna da yawa sunji mugan ciwuka

- Harin wanda aka kai shi da asubar farin yau yayi sanadiyyar raba mutaane da dama daga gidajen su domin tsira da rayukan su

Mutane shida ciki hadda wata tsohuwar mace sun rasa rayukan su, a wani hari da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai garin Tsondi dake karamar hukumar Wukari jihar Taraba.

Majiyarmu Legit.ng ta samo rahoton cewa maharan sun shiga kauyen da asubar fari inda suka harbi mutane masu yawan gaske.

Mun samu rahoton cewa mutane shida ne suka rasa rayukan su a lokacin da suka kai harin sannan kuma da yawa suka ji raunuka sanadiyyar taba su da harsashi yayi.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun fito daga jihar Binuwai ne, wacce ke makwabtaka da jihar ta Taraba inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi akan kabilar Jukun din.

KU KARANTA: Mijina yana saduwa da wata mahaukaciya - Wata mata ta nemi kotu ta raba aurensu

Bayan haka kuma maharan sun sanyawa gidaje da yawan gaske wuta, inda suka tilastawa al'ummar garin yin hijira suna komawa cikin garin Wukari da wasu kauyuka da suke makwabtaka da su domin tsira da rayukansu.

Yankin da kauyen Tsondi yake sun sha samun hare-haren 'yan bindiga sama da wata daya da ya wuce, hakan yayi sanadiyyar sace mutane da dama da kuma kone kauyuka kimanin guda 10.

A yanzu haka dai an kai mutane biyar asibiti domin karbar magani sanadiyyar raunukan da suka samu sakamakon harin.

Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar DSP David Misal ya ce bashi da masaniya akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel