Buhari ya yi alhinin mutuwar Francis Johnson

Buhari ya yi alhinin mutuwar Francis Johnson

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar Shugaban Kungiyar Manyan Ma'aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta kasa (PENGASSAN), Francis Johnson a ranar Juma'a.

A sanarwar da hadiminsa na fanin kafafen yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya mika ta'aziyarsa ga PENGASSAN da dukkan kungiyoyin kwadago na kasa bisa rasuwar Johnson wanda ya bayyana a matsayin 'shugaba mai hangen nesa'.

Shugaban kasar ya tabbatar da kyawawan halayen Johnson da kuma jajircewarsa wurin ganin ya inganta walwala da jin dadin ma'aikata da kuma gudunmawar da ya bayar wurin dai-daita fanin man fetur a kasar.

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Ya ce hikima da rashin son abinda duniya da kishin kasa na marigayin ya taimaka sosai wuri ganin ba a samu matsala ba tsakanin ma'aikatan man fetur da wadanda su ke yi wa aiki.

A cewarsa, rasuwar shugaban kungiyar babban rashi ne ga iyalansa da kungiyoyin kwadago da kasar baki daya.

Shugaban Buhari ya yi addu'ar Allah ya gafartawa marigayin ya kuma bawa iyalansa ikon jure rashinsa kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel