Gwamnonin arewa na goyon bayan Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa

Gwamnonin arewa na goyon bayan Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa

-Tawagar kamfe ta Femi/Wase ta kai yakin neman zabenta arewacin Najeriya inda gwamnonin jihohin suka nuna goyon bayansu ga dan takarar dari bisa dari.

-Abdulmumin Jibrin shi ne ya jagoranci tafiyar wacce ke dauke da yan majalisa sama da mambobi 120.

Yayin da majalisar dokoki ke shirin nadin sabbin shugabanni a ranar 11 ga watan Yuni, wasu daga cikin gwamnonin arewa sun goyi bayan shugaban masu rinjaye na majalisar wato Femi Gbajabiamila na ya kasance kakakin majalisar ta 9.

Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna da takwaransa na jihar Borno Babagana Zulum ne suka bayyana a fili cewa suna goyon bayan takarar Femi/Wase a matsayin kakaki da mataimakinsa yayin da tawagar kamfe dauke da yan majalisa sama da 120 ta kai masu ziyara a jihohinsu.

KU KARANTA:‘Yan sanda sun kama mutum 12 da ake zargi da laifin fashi da kuma garkuwa da mutane a Jigawa

Gwamnonin sun ce, Gbajabiamila tare da abokin takararsa Idris Wase na da kwarewa ta gaske wurin tafiyar da al’amuran majalisar dokoki. Wannan dalilin ne ya sanya suka kasance a kan gaba kuma mafi dacewa da wannan jagoranci.

A cewar El-Rufai kamar yadda mutane da dama ke tunanin cewa Tinubu ne ya tsaida Gbajabiamila wannan maganar ba haka take ba, shugaba Buhari ne da kansa ya fiddo shi a matsayin dan takarar kakakin majalisa saboda kwarewarsa fagen aikin majalisa.

Sarkin yakin neman zaben Femi/Wase wato Abdulmumin Jibrin (Kano, APC) ya shaidawa gwamnan Borno cewa tawagar tasu ta kamfe ta fara zuwa jihar Kaduna kafin isowarsu Borno. Dalilin zuwansu Kaduna kuwa shi ne domin gwamna El-Rufai ya sanya albarka wa dan takarar na su.

Daya daga cikin masu neman kujerar kakakin majalisar, Abdulrazak Namdas (APC, Adamawa) ya janye takararsa inda ya shigo tsundum cikin tafiyar Femi Gbajabiamila kai tsaye.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel