Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun karamar sallah

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun karamar sallah

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da Talata, 4 ga watan Mayu da Laraba, 5 ga watan Mayu a matsayin ranakun hutu domin bikin karamar sallar.

Sakatariyar din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Barista Georgina Ekeoma Ehuriah ta sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu ta hannun Daraktan labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Mohammed Manga.

Ta taya Musulmai murnar kammala azumin Ramadana cikin nasara sannan ta bukaci dukkanin yan Najeriya da suyi amfani da bikin wajen addu’an zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da daidaitar kasar.

Ta bukaci yan Najeriya da su guji kalamun kiyayya da hada hannu da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen Gina zaman lafiya, da hadin kai mai karfi a Najeriya domin cika cigaban da ke kunshe da mataki na gaba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Anyi harbe-harbe a Kaduna yayinda yan sanda suka tarwatsa yan Shi’a dake zanga-zanga

Barista Ehuriah ta sake ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya ya jajirce domin kare yan Najeriya, inda ta kara da cewa hukumomin tsaro, a karkashin ma’aikatar sun yi umurnin tabbatar da samar da ingantaccen tsaro a lokaci da bayan bikin Sallah.

Ta kuma jadadda cewa gwamnatin tarayya na fatan dukkanin yan Najeriya za su ci gaba akan koyarwar wata mai tsarki ta hanyar yin Sada ka, da soyayyar juna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel