‘Yan sanda sun kama mutum 12 da ake zargi da laifin fashi da kuma garkuwa da mutane a Jigawa

‘Yan sanda sun kama mutum 12 da ake zargi da laifin fashi da kuma garkuwa da mutane a Jigawa

-Jami'an yan sanda a jihar Jigawa sun yi nasarar damke mutane 12 masu aikata laifukan fashi da kuma garkuwa da mutane a fadin jihar.

-Kwamishinan yan sandan jihar Bala Senchi ne ya bada wannan sanarwa a Dutse a babban birnin jihar Jigawa.

Mutane 12 a jihar Jigawa sun shiga hannun jami’an yan sanda inda ake zarginsu da laifin fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma mallakar muggan makamai ba bisa ka’ida ba. Kwamishinan yan sandan jihar Bala Senchi ne ya bada wannan sanarwa.

Senchi ya ce mutum 7 daga cikin wadanda aka damke an same su ne da laifin fashi da makami, kwace da kuma wasu miyagun laifuka masu kama da wadannan.

KU KARANTA:Buhari ne ya zabi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa ba Tinubu, inji El-Rufai

Ya sake bayyana mana cewa, an kama mutanen ne ranar 6 ga watan Mayu bayan da rundunar jami’ansu ta kai wani samame gidan wani Dan’azumi a Madobi dake karamar hukumar Dutse. An same shi da tsabar kudi N500,000 tare da muggan makamai.

Kwamishinan ya shaidawa manema labarai cewa an kama mutanen ne a wurare daban daban sai dai laifukansu na kama dana juna.

“Daga cikin abubuwan da aka karbe daga hannun wadanda aka kama akwai turamen zani guda 45, shadda yadi 12, gyale 2, babur, mabudi na musamman da kuma lambar da ake sanyawa abun hawa da bindigogi irin daban daban da albarushi.” Inji kwamishinan.

Bugu da kari, kwamishinan ya jaddada kudurin hukumarsu na kawo karshen ta’addanci a jihar Jigawa. Kana kuma ya shaidawa manema labarai cewa nan ba da jimawa ba za’a aika da masu laifin kotu domin fuskantar shari’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel