Rigakafin cutar shan inna a Kebbi ta faranta ran uwargidan gwamna Bagudu

Rigakafin cutar shan inna a Kebbi ta faranta ran uwargidan gwamna Bagudu

-Dakta Zainab Shinkafi Bagudu tayi murna akan nasarar rigakafin cutar shan inna a jihar Kebbi.

-Rigakafin cutar shan inna ya samu kari daga kashi 18 zuwa kashi 74 cikin dari a jihar Kebbi, kamar yadda uwargidan gwamnan jihar Kebbin ta fadi.

Dakta Zainab Shinkafi Bagudu uwargidan gwamnan jihar Kebbi ta bayyana jin dadinta game da cigaba da rigakafin cutar shan inna ke samu a jihar Kebbi inda aka samu kari daga kashi 18 cikin dari zuwa kashi 74 a yanzu.

Dakta Zainab ta bayyana farin cikinta a fadar gwamnatin jihar Kebbi yayin da take taya maigidanta da kuma shugaba Buhari murnar rantsar da su da akayi a ranar 29 ga watan Mayun 2019.

Cigaba a fannin rigakafin cutar shan inna a Kebbi ya faranta ran uwargidan gwamna Bagudu

Dakta Zainab Atiku Bagudu
Source: Facebook

KU KARANTA:Buhari ne ya zabi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa ba Tinubu, inji El-Rufai

Ta ce, a lokacin da maigidanta ya hau mulkin jihar shekaru hudu da suka wuce rigakafin na samun kashi 18 ne cikin dari kacal.

“ A lokacin da muka shigo gwamnati ilahirin rigakafin da akeyi a fadin jihar nan na tsakanin kashi 17 zuwa 18 ne a cikin dari.

“ Kungiyar likitocin kananan yara ta kasa suka zo jihar nan, su ka ce mani ya za’ayi a ce rigakafin ta tsaya a kashi 18 kawai cikin dari duk da cewa ina jihar.” A cewarta.

Dakta Bagudu wacce ita ce ta kafa gidauniyar Medicaid domin masu cutar kansa, ta ce nasarar da aka samu a jihar Kebbi ta bangaren rigakafin shan inna abin murna ne.

Ta yi godiya ta musamman ga masu ruwa da tsaki wurin cinma wannan babbar nasara, kamar hukumar kula da lafiyar jihar Kebbi, kungiyar lafiya ta duniya wato WHO da kuma kungiyar UNICEF.

A karshe kuma ta yi godiya da jinjina ga maigidanta gwamna Abubakar Atiku Bagudu bisa irin goyon bayan da yake bai wa sashen kiwon lafiya na jihar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel