Wani babban jigon PDP da magoya bayansa sun sauya sheka zuwa APC

Wani babban jigon PDP da magoya bayansa sun sauya sheka zuwa APC

Wani dan takaran majalisan wakilai a majalisan People’s Democratic Party (PDP) a zaben kasa da ya gabata, Mista Olakunle Ojo, da magoya bayansa, sun sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Farfesa Afolabi Ojo, ya sauya sheka a Ward 11 a Ado Ekiti, a ranar juma’a, 31 ga watan Mayu.

Yace ya yanke shawaran ne, saboda tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ta ci amanar al’umma saboda haka bai ga amfani da cigaban da zai iya samu ba a harkarsa na siyasa da kuma na magoya bayansa.

Daga cikin wadanda suka karbi bakuncinsa sun hada da mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Hon. Sola Elesin, shugaban APC,na karamar hukumar Ado, Hon. Mike Akinleye da shugaban jam’iyyar a Ward 11, Mista Adegoke a madadin kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda Hon Paul Omotosho ke shugabanta.

Yayin da yake magana a madadin kwamitin, Elesin, yace zaben gwamna na 2022 zai zo ma jam’iyyar da sauki idan Fayemi ya kammala aiwatar da ajendansa guda hudu.

Yace yana yiwuwa gwamnan yayi nasarar yin haka idan jam’iyya mai mulki ta daidaita hadin kai tsakanin mambobi.

K KARANTA KUMA: Eid Al Fitr: UAE ta kafa kwamitin neman wata domin tabbatar da karshen Ramadan

Shugaban APC, a karamar hukumar Ado, Mista Mike Akinleye yace wadanda suka sauya shekar za su ga gata kamar yadda ake nuna wa tsoffin mambobin jam’iyyar.

Ya bukace su da su yi amanna da kwarewar gwamna Kayode Fayemi wajen inganta arzikin jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel