Yanzu-yanzu: Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar kan Sabon Alkalin Alkalai

Yanzu-yanzu: Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar kan Sabon Alkalin Alkalai

Wata babbar kotun tarayya dake zaune a unguwar Jabi na birnin tarayyar Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar kan mukaddashin shugaban Alkalan Najeriya, Muhammad Tanko, kan zargin rage shekarunsa.

Wanda ya shigar da kara, Mista Tochi, ya yi zargin cewa mukaddashin CJN, Tanko Mohammed, ya rage shekarunsa da shekaru uku inda yayi bayanin cewa an haifi Alkalin ranar 31 ga Disamba, 1950 amma yana amfani da 31 ga Disamba, 1953.

Alkalin kotun, Danlami Senchi, yayin yanke hukuncin a ranar Juma'a ya ce wanda ya ke zargin bashi da hurumin shigar da irin wannan kara saboda bai yi bayanin yadda wannan zargi zai shafi aikinsa ko yan Najeriya ba.

KU KARANTA: Yan sanda sun gano kokon kan wani magidanci a cikin motarsa

Kotun ta kara da cewa Mista Tochi bai yi bayanin yadda ya samu wannan labari na cewa Alkali Tanko Mohammed ya rage shekarunsa ba saboda bai gabatar da wata hujja gaban kotu ba.

Alkali Danlami Senchi ya wannan kara da aka shigar kawai kokarin cin mutuncin mukaddashin Alkalin alkalan Najeriya ne da yi masa sharri.

Kafin watsi da karar, Ya yi kira ga magatakardan kotun kolin Najeriya da ta dau tsattsaurin mataki kan lauyan Mista Tochi, Melkizadeck Zaro, kan nuna rashin kwarewa wajen aiki.

Inji shi, hakan na iya kawo batanci ga bangaren shari'a kuma ba za'a yi hakuri da wannan dabi'a ba.

A karshe, kotun ya umurci Mista Tochi ya biya alkalin alkalai kudi milyan goma kan zargin karya, kuma wajibi ne ya biya cikin makonni uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel