Yayan majalisar dokokin jahar Imo sun zabi sabon kaakakin majalisa

Yayan majalisar dokokin jahar Imo sun zabi sabon kaakakin majalisa

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Onuimo ta jahar Imo, Chinedu Offor ya zama sabon shugaban majalisar dokokin jahar Imo, watau Kaakakin majalisa, bayan murabus din da tsohon kaakakin majalisar, Lawman Duruji.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Duruji a ranar Talata, 28 ga watan Mayu ne aka zabi Duruji a matsayin sabon kaakakin majalisar bayan tsohon kaakakin Acho Imo yayi murabus, amma sai gashi yayi murabus bayan kwanaki biyu a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Sabon gwamna ya fara da biyan ma’aikatan albashinsu

Yayan majalisar dokokin jahar Imo sun zabi sabon kaakakin majalisa

Offor
Source: Twitter

A ranar Talatar data gabata ne aka gudanar da zaben kaakakin majalisar, inda Duruji ya samu kuri’u 14, ya kayar da Chinedu Offor a gogoriyon zama kaakakin majalisar wanda ya samu kuri’u 11.

Sai dai bayan yin murabus da Duruji yayi, hakan ya baiwa Offor daman sake neman kujerar kaakakin majalisar, kuma aka yi sa’a babu wanda ya tsaya takara dashi, inda a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu aka zabeshi a matsayin sabon kaakaki.

Amma kuma wani hanzari ba gudu ba, shi kansa sabon kaakakin majalisa Offor ba zai dade akan mukamin ba sakamakon bai samu nasara a kokarinsa na yin tazarce a kujerarsa ba, inda ya sha kashi a zaben 2019 duk da ya tsaya takara a sabuwar jam’iyyarsa ta Action Alliance.

A shekarar 2015 ne aka zabi Offor zuwa majalisar dokokin jahar Imo a karkashin inuwar jam’iyyar APC tare da tsohon gwamnan jahar Rochas Okorocha, amma daga bisani ya sauya sheka zuwa AA, haka zalika ya taba zama kaakakin tsohon Gwamna Rochas Okorocha, da kuma kwamishinan watsa labaru a gwamnatinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel